Monday 26 January 2026 - 07:05
Iran Tana Cikin Cikakkiyar Kwanciyar Hankali; Kafofin Watsa Labaran Yamma Karya Suke Yadawa 

Hauza/ Hujjatul Islam wal-Muslimin, Abdulmajid Hakim Elahi, a wani jawabi da ya yi na kin amincewa da karyar da kafafen yada labarai ke yaɗawa, ya jaddada cewa Iran tana cikin cikakkiyar kwanciyar hankali, kuma ana sarrafa munanan yan fitina yadda ya kamata.

Sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza ya bayar da rahoton cewa, Hujjatul Islam wal Muslimin Abdulmajid Hakim Elahi wakilin Waliyul Faqih a kasar Indiya yayin da yake ishara da yadda kafafen yada labarai suka kirkiri tashe-tashen hankula a Iran ya ce: "Abin da ake yadawa a kafafen yada labarai na duniya da shafukan sada zumunta ba ya nuna hakikanin hakikanin abin da ke faruwa a cikin kasar Iran, kuma galibi an tsara shi ne ta hanyar farfaganda da aka tsara.

A ci gaba da jawabin nasa ya banbance tsakanin abubuwan da ke faruwa a kasa da kuma labaran da wasu 'yan jarida da kungiyoyin 'yan adawa da makiya Iran suka kirkira kuma suke magana akai, ya kuma bayyana cewa akwai tazara mai zurfi tsakanin gaskiya da tatsuniyoyi, kuma abin da ake bugawa a matakin duniya a yau bai dace da hakikanin yanayin da ake ciki a Iran ba.

Wakilin Waliyul Faqih a kasar Indiya ya kuma yarda da samuwar matsalolin tattalin arziki ya kara da cewa: "Wadannan kalubalen ba wai gazawar cikin gida ne ke haifar da su ba, illa dai sakamakon yakin tattalin arziki da aka shirya kai tsaye da aka shafe shekaru da dama ana gwabzawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran."

A ci gaba da bayanin nasa ya ce: "Eh, akwai matsalolin tattalin arziki, kuma abu ne na dabi'a cewa wasu mutane ba su ji dadin wannan lamari ba, to amma wadannan matsalolin na faruwa ne sakamakon takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa Iran."

Hujjatul Islam wal-Muslimin Hakim Elahi ya yi gargadin cewa wasu mutane masu neman dama cikin sani suna yin mummunan amfani da matsalar tattalin arziki don haifar da rashin kwanciyar hankali da ci gaban manufofinsu na siyasa. Sannan ana kara girman zanga-zangar takaitacciya da take a warwatse da gangan don nuna hoton karya na tashe-tashen hankula a kasar baki daya.

Ya kuma yi fatali da kakkausar murya kan wuce gona da iri da ake yadawa a shafukan sada zumunta tare da jaddada cewa halin da ake ciki a Iran gaba daya yana karkashin kulawa.

Wakilin Waliyul Faqih ya ci gaba da cewa: "A halin yanzu yanayin yana da kyau sosai, kuma yana cikin kwanciyar hankali, kuma abin da ake tattaunawa a shafukan sada zumunta bai ma kusa da hakikanin abin da ke faruwa a wannan fanni ba."

A karshe ya jaddada cewa, duk da tsauraran takunkumai da matsin lamba daga waje, Iran na ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali, tsari da tsayin daka na jama'a; Gaskiyar da ta saba wa gurbatattun hotuna da ake yadawa a kasashen waje.

Yana da kyau a san cewa kalaman wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a Indiya sun kalubalanci babban labarin kasa da kasa da ke nuna Iran tana a cikin matsala. Kuma wadannan karairayin na kafofin watsa labarai wani bangare ne na yakin tunani da yada labarai da nufin raunana da kuma bata sunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha